6 Satumba 2015 - 18:29

Tun bayan da aka kashe sojojin hadaddiyar daular laraba dake aiki tare da dakarun hadinguiwa da kasar saudiya wajen kai hari kan fararen hula a kasar Yaman ne da dama daga cikin Alummar kasar suke ta kiraye-kirayen na a janye sojojin kasar , tare da bukatar gwamnatin kasar da ta yi musu bayani game da makomar yayansu,

 Al’ummar Hadaddiyar Daular Larabawa sun ci gaba da kiraye-kirayen janye sojojin kasar daga kasar Yaman da suka kira ta da Viyatanam.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan yaduwar labarin kashe sojojin kasar guda 45 a kasar Yaman da dama daga cikin Alummar kasar suke ci gaba da kiraye-kirayen na bukatar gwamnatin kasar da ta janye dukkan sojojin kasar daga kasar Yaman,

A gefe guda kuma wasu rahotanni sun nuna cewa dubban daruruwan Alummar kasar ne suka bazama akan titunan kasar domin yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da ci gaba da zaman sojojin kasar a kasar Yaman tare da yin kira ga gwamnatin kasar da ta bayyana musu halin da yayansu suek ciki a kasar Yaman tare da bukatar a dawo musu da yayansu gida,

Hadaddiyar daular larabawa ta aike da sojojinta zuwa kasar Yaman ne karkashin dakarun hadin guiwa da kasar Saudi Arebiya ke jagoranta a ci gaba da akai hare-hare na wuce gona da iri kan fararen hula da mata da yara kanana288.